Wannan wata tattaunawa ce mai armashi da ta ja hankalin jama’a, wanda mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Babban Mai Bai ...
Wannan wata tattaunawa ce mai armashi da ta ja hankalin jama’a, wanda mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Babban Mai Bai wa Gwamnan Shawara na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai, Sulaiman Bala Idris ya yi, inda ya bayyana ƙwarewa da jajircewa wajen fayyace matsayar gwamnatin jihar kan zargin sace wani hadimin gwamnan.
Hirar ta gudana ne a shirin nan na musamman na SUNRISE DAILY na gidan talabijin na CHANNELS, inda kakakin gwamnan ya nuna basira, natsuwa da iya warware batutuwa masu sarƙaƙiya cikin hikima da hujjoji masu ƙarfi. Ta hanyar amsoshinsa masu gamsarwa. Idris ya sake tabbatar da kansa a matsayin kakaki nagari, mai kare gaskiya da muradun jama’a, tare da bayyana ƙudurin Gwamnatin Zamfara na fuskantar duk wani ƙalubale da ke addabar jihar.
Inda za a iya tunawa a ranar 7 ga watan Janairun nan, Gwamnatin Jihar Zamfara ta fitar da wata sanarwa mai ɗaukar hankali, inda ta ce Ƙaramin Ministan Tsaro na amfani da ofishin Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) wajen tsangwama da barazana ga ’yan adawa a jihar. Gwamnatin ta bayyana cewa ta kai ga fitar da wannan sanarwa ne saboda tsananin damuwa kan yadda ake amfani da ƙarfin gwamnati wajen gallaza wa ’yan adawa da Gwamnatin Tarayya a Zamfara.
A cewar gwamnatin jihar, ba su da wani zaɓi face su fito fili su sanar da al’umma yadda Ƙaramin Ministan Tsaron ke amfani da ofishin NSA wajen razana ’yan adawa, tare da yin amfani da jami’an tsaro domin cimma muradunsa.
Ga yadda hirar ta kasance;
CHANNELS: Mun gode ƙwarai da kasancewarka tare da mu a safiyar yau. Barka da safiya.
IDRIS: Na gode sosai da gayyata ta.
CHANNELS: Mene ne ainihin wannan zargi da ku ka yi. Wace irin tsangwama ce ku ka lura da ita har ta kai ga fitar da wannan sanarwa?
IDRIS: Idan za ku tuna, a ’yan watanni ko makonnin baya, an samu wasu bidiyo da dama na wani Malami daga jihar Sakkwato yana zargin Ƙaramin Ministan Tsaro da hannu a harkokin ’yan bindiga. Mutane da yawa sun riƙa yaɗa waɗannan bidiyoyi a shafukan sada zumunta, musamman a Twitter (X), inda ake kira ga Shugaban Ƙasa da ya ɗauki mataki, ko ya binciki Ministan bisa zargin da ake masa.
Wani hadimi a ofishina, Salim Abubakar, wanda ke aiki a matsayin mataimaki a fannin fasaha, shi ma ya wallafa wannan bidiyon a shafinsa na X. Abin takaici, a makon jiya Laraba, Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle ya aike da jami’an tsaro suka sace wannan hadimin a nan Abuja. A lokacin ba mu san inda aka kai shi ba.
Mun fara bincikenmu, muna neman labari ta hannun majiyoyinmu, har sai da muka gano cewa an kai shi wani ofishin ’yan sanda a tsakiyar ƙwaryar Abuja, kusa da Ma’aikatar Ilimi. Abin da suka yi da farko shi ne sun ɓoye inda suka kai shi domin kada kowa ya sani. Amma mun samu bayanai daga majiyoyinmu cewa a can aka tsare shi.
Da muka isa ofishin ’yan sandan, muka tambayi DPO dalilin tsare Salim. Sai ya ce an kawo shi daga ofishin Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro NSA ne domin “ajiya ta tsaro”. Muka tambaye shi, daga ofishin NSA? Ya ce eh, daga can aka kawo shi.
CHANNELS: To ta yaya hakan ya shafi Ministan Tsaro?
IDRIS: Mun sake zurfafa bincike. Mun tuntubi wasu mutane a ofishin NSA, suka ce ba su san komai ba, kuma ofishinsu bai da hannu a wannan lamarin. Amma a wannan lokaci, DPO na cewa daga ofishin NSA aka kawo Salim.
Washegari muka tafi ofishin ’yan sandan tare da wani babban jami’i daga ofishin NSA da kuma wani babban lauya. A lokacin da muka isa, DPO ya sake sauya labari. Jami’in NSA da muka tafi da shi bai bayyana kansa da farko ba. Amma DPO ya ce jami’an tsaro daga ofishin NSA ne suka kawo Salim.
Sai jami’in ya tambaye shi, “Ka san ni?” Ya ce a’a. Sai jami’in ya ce, “Ni jami’i ne daga ofishin NSA.” Nan take DPO ya sauya magana, ya ce, “A’a, ba daga ofishin NSA aka kawo shi ba. Ministan Tsaro ne ya kawo shi.”
CHANNELS: Amma ba ku je wajen Ministan Tsaro kai tsaye ba?
IDRIS: Bayan jami’in NSA ya bayyana kansa, ya umurci DPO da ya saki Salim nan take, saboda sun yi amfani da sunan ofishin NSA ba tare da izini ba.
CHANNELS: Bari na miƙa tambaya zuwa ga abokin aikina Ayo da ke ofishin mu a Legas.
CHANNELS Ayo: Na gode. Malam Idris, kasancewarka a nan yana nuna cewa kana da ƙwarin gwiwar cewa abin da hadiminku, Salim Abubakar, ya wallafa gaskiya ne. Bidiyon da ya wallafa na wani mutum ne yana zargi. Shin gwamnatin Zamfara tana da hujjar da za ta tabbatar da gaskiyar abin da Malamin ya faɗa?
IDRIS: Ba Gwamnatin Zamfara kaɗai ba, har Gwamnatin Tarayya ma na da hujjoji idan suna son su fito da gaskiya.
CHANNELS: Bari mu fara da gwamnatin jihar. Shin kuna da hujjar da ke nuna cewa Ministan Tsaro yana da hannu a harkokin ’yan bindiga?
IDRIS: Akwai wani bidiyo na tsohon mataimakin Matawalle wanda ya bayyana abubuwa masu yawa. Wannan bidiyo hujja ce ƙarara, kuma ya yaɗu sosai a shafukan sada zumunta. Haka kuma, ina tabbatar maka cewa gwamnatin tarayya na da waɗannan hujjoji.
CHANNELS: Kowa na iya yin zargi. Amma idan ba tare da hujja ba, ba za a iya kaiwa kotu ba. Idan kun tabbatar da cewa abin da Salim ya wallafa gaskiya ne, shin kun rubuta wa ’yan sanda takardar ƙorafi? Domin idan Ministan ya kai ƙara, ’yan sanda na da ikon ɗaukar mataki. Shin ku ma kun kai ƙara ga ’yan sanda?
IDRIS: Abin da aka yi wa Salim ba kame ba ne, sace shi aka yi. Ba a kama shi bisa doka ba. An rufe masa ido, dukkan jami’an tsaron suna sanye da abin rufe fuska. Sun kai shi wani wuri da ba mu sani ba.
Mun kai rahoto ga ’yan sanda, shi ya sa muka samu bayanin inda aka tsare shi. Idan da Ministan yana da gaskiya, ya kamata ya kai shi kotu tun farko, ba wai ya sace shi ba. Amma mun yi bincike sosai har muka gano inda aka kai shi.
A ranar Juma’a, bayan jami’an NSA sun umurci DPO da ya sake Salim, sai aka tafi da shi kotun majistare a Asokoro. Lauyoyinmu sun nemi beli, amma Alƙalin kotu ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga wata, wato yau ke nan.
Matawalle ba shi da wata hujja ta gaskiya. Idan yana da hujja, ya kamata ya je kotu ne, ba wai ya sace mutum ba.
CHANNELS: Ka ce sace shi aka yi. Shin kun kai rahoton satar ga ’yan sanda? Yanzu da lamarin ke gaban kotu, me ku ke fata?
IDRIS: Ina so in tambaye ka, daga ina ka ke tunanin muka samu bayanin cewa Salim yana ofishin ’yan sanda na Central Area? Daga ’yan sanda ne. Mun kai rahoton sace mutum, suka yi bincike, suka ba mu bayanin inda aka tsare shi.
DPO yana hulɗa kai tsaye da Matawalle. Ba magana ce kawai ba, muna da hujjoji. A lokacin da muka koma can, mutanen Matawalle suna kiran DPO kai tsaye. DPO ya gaya wa iyayen Salim cewa Ministan na da wasu buƙatu: Salim ya rubuta takardar neman afuwa a shafinsa na X, sannan ya miƙa mubaya'a ga Matawalle, tare da alƙawarin ba zai sake rubuta komai a kansa ba.
Waɗannan hujjoji ne da ke nuna hannun Matawalle dumu-dumu. Ta yaya za ka tilasta wa mutum ya rubuta neman afuwa idan ba ka da wani abin ɓoyewa?
CHANNELS: Mun fahimci cewa Ministan Tsaro ya kai ƙara kotu. Gaskiya ne?
IDRIS: Eh.
CHANNELS: Wa ya kai ƙara a kansa?
IDRIS: Ya kai ƙara kan Salim ne, saboda mun fallasa shi. Mun kai jami’an da ya yi amfani da su, sunan ofishin NSA, zuwa ofishin ’yan sanda.
CHANNELS: Amma ofishin NSA ya musanta ai?
IDRIS: Haƙiƙa, saboda ba su da hannu. Mun kai ƙara ofishinsu, shi ya sa suka musanta. Amma Matawalle da ’yan sanda sun ƙi saurare.
CHANNELS: Ta yaya ka ke ganin za a warware lamarin?
IDRIS: Ya kamata shugaban NSA, Malam Nuhu Ribadu, ya hana Matawalle amfani da jami’ansa wajen tsangwamar mutane. Matawalle ya taba tsangwamar ’yan jaridar VISION FM, LIBERTY Radio. Wannan ba mulkin kama karya ba ne. Ba za a yarda mutum guda ya riƙa gallaza wa jama’a ba.
CHANNELS: Mun gode ƙwarai da zuwanka.
IDRIS: Nima na gode.
No comments