Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa ’yan bindigar da suka ƙi zaman lafiya tare da ci gaba da barazana ga rayukan...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa ’yan bindigar da suka ƙi zaman lafiya tare da ci gaba da barazana ga rayukan jama’a, musamman a jihar Zamfara dole ne su fuskanci hukunci bisa tanadin doka, babu maganar sulhu da su.
Gwamnatin Jihar Zamfara ta karɓi baƙuncin wani taron tsaro na musamman kan Arewa maso Yamma, wanda Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta shirya, kuma aka fara gudanar da shi ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau.
A wata sanarwa da Sulaiman Bala Idris Mai Magana Da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara ya raba wa manema labarai a Gusau, ta bayyana cewa an shirya taron na tsawon kwanaki uku ne da taken “Nazarin Ƙalubalen Tsaro a Yankin Arewa maso Yamma”, tare da halartar Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu.
Taron ya haɗa manyan jami’an Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, wakilan gwamnatocin jihohin Arewa maso Yamma, shugabannin hukumomin tsaro da leƙen asiri, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da ƙungiyoyin fararen hula.
Da yake buɗe taron, Gwamna Lawal ya yaba wa Sufeto Janar na ’Yan Sanda da shugabancin Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya bisa shirya taron da kuma zaɓar Zamfara a matsayin jihar da za ta karɓi baƙuncinsa.
Ya ce, zaɓar Zamfara na da muhimmanci saboda jihar na ɗaya daga cikin wuraren da matsalar tsaro ta fi tsanani a Arewa maso Yamma.
A cewarsa, wannan ya sa jihar ta dace da gudanar da cikakken nazari kan matsalolin tsaro da kuma samar da hanyoyin magance su.
Lawal ya ce, matsalar tsaro a yankin ba ta tsaya kan aikata laifuka na yau da kullum ba, domin ƙungiyoyin masu aikata laifuka suna gudanar da garkuwa da mutane da satar shanu a tsakanin iyakokin jihohi.
Ya ce, hakan na barazana ga rayuwar jama’a, samar da abinci, ilimi, zuba jari da zaman lafiyar al’umma.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa akwai wasu barazanar tsaro a birane, ciki har da ta’addancin ’yan daba, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kutsen masu tsattsauran ra’ayi.
A cewarsa, irin wannan yanayi na buƙatar a daina amfani da martanin tsaro da ya rabu-rabu, domin masu aikata laifuka ba sa kallon iyakokin jihohi.
“Dole tsarin tsaronmu ya kasance haɗe wuri guda. Bayanan sirri daga Zamfara na iya hana hari a wata jiha, haka kuma ayyukan tsaro a makwabciyar jiha na iya daƙile barazanar da ke fuskantar Zamfara,” inji shi.
Ya ce yankin na buƙatar ingantattun hanyoyin musayar bayanan leƙen asiri cikin gaggawa, gudanar da ayyukan tsaro tare, sa ido tsakanin jihohi, aikin ’yan sanda na haɗin gwiwa da al’umma, da kuma ci gaba da katse hanyoyin kuɗi, kayayyaki da kayan aiki da ke taimaka wa ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
Lawal ya ce taron ya tattaro wasu daga cikin ƙwararrun jami’an Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro wajen dabarun aiki da tattara bayanan sirri.
Ya buƙaci mahalarta su tashi daga Gusau ba tare da taƙaita taron ga sake bayyana matsalar rashin tsaro ba, sai dai su fito da matakan da za a iya aiwatarwa nan take.
Ya ce ya kamata a samar da hanyoyin da za su katse hanyoyin samar da kayayyaki ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka tare da takaita zirga-zirgarsu.
Ya bayyana cewa ƙungiyoyin masu aikata laifuka suna dogaro da hanyoyin sufuri, kasuwanni, masu shiga tsakani, masu ba da kuɗi da kuma wasu cibiyoyin tallafi.
Saboda haka, ya ce akwai buƙatar amsa muhimman tambayoyi kan yadda za a katse hanyoyin samar musu da kayayyaki, takaita motsinsu a dazuzzuka, ƙauyuka da kan iyakoki, tare da ƙara tsaro a wuraren da ke da rauni ba tare da hana harkokin kasuwanci na halal ba.
Haka kuma, ya nemi a gano tare da wargaza hanyoyin masu ba da bayanai da masu taimaka wa masu aikata laifuka.
A nasa jawabin, Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya ce tabbatar da tsaron Arewa maso Yamma alhakin kowa ne, saboda muhimmancin yankin ga Nijeriya.
Ya ce hukumomin tsaro sun haɗa ƙarfi tsakanin jihohi domin tunkarar matsalar rashin tsaro, tare da yin sintiri tare da musayar bayanan sirri.
Disu ya ce rundunar ta yanke shawarar kai farmaki ga masu aikata laifuka maimakon ci gaba da jiran hare-harensu.
“Mun yanke shawarar tunkarar waɗannan masu aikata laifuka. Wannan ne ya sa muka kira wannan taro,” inji shi.
Sufeto Janar ya kuma tabbatar da cewa Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya za ta ci gaba da amfani da ƙarfinta, jami’anta da haɗin gwiwarta da sauran hukumomi wajen tabbatar da tsaron yankin.
Sai dai ya jaddada cewa aikin ’yan sanda ya fi samun nasara idan jama’a suka ba da cikakken goyon baya da haɗin kai.
No comments