Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya raba sabbin motocin aiki ga manyan makarantun gaba da sakandare da wasu hukumomin ilimi n...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya raba sabbin motocin aiki ga manyan makarantun gaba da sakandare da wasu hukumomin ilimi na jihar, a wani mataki da ya ce zai ƙara inganta ayyuka da tafiyar da harkokin ilimi.

An gudanar da rabon motocin ne ranar Juma’a a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce motocin mallakar hukumomi ne, kuma za a yi amfani da su wajen gudanar da harkokin gudanarwa da ayyuka, sa ido kan ayyuka, tantance makarantu, halartar ayyukan hukuma da sauran nauyin da ya rataya kan cibiyoyin da suka amfana.
Cibiyoyin da aka ware wa sabbin motocin sun haÉ—a da Jami’ar Tarayya ta Gusau, Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara, da Kwalejin Fasaha ta Abdu Gusau da ke Talata Mafara.

Sauran waÉ—anda suka amfana sun haÉ—a da Kwalejin Koyar da Aikin Jinya da Ungozoma ta Gusau, Hukumar Kula da Ayyukan Malamai, Hukumar Kula da Makarantun Sakandare, Sashen Tabbatar da Ingancin Ilimi, Kwalejin Nazarin Larabci da Shari’a ta Zamfara (ZACAS), da sauran cibiyoyin gwamnati na jihar.
Da yake jawabi yayin rabon motocin, Gwamna Lawal ya ce matakin zai taimaka wajen Æ™ara Æ™wazo da ingancin ayyukan jami’an gwamnati, musamman ta hanyar samar musu da hanyoyin sufuri masu inganci da za su ba su damar gudanar da ayyukansu cikin sauri da sauÆ™i.

Gwamnan ya jaddada cewa motocin ba mallakar kowane jami’in gwamnati ba ne, sai dai dukiyoyin Gwamnatin Jihar Zamfara ne da aka bayar domin ayyukan hukuma.

Ya ce, “Ya kamata a fahimci cewa waÉ—annan motocin ba wani haƙƙi ne na Æ™ashin kai da wani jami’in gwamnati zai mallaka ba. Dukiyoyin Gwamnatin Jihar Zamfara ne, kuma dole ne a yi amfani da su yadda ya kamata, musamman wajen gudanar da ayyukan hukuma kawai.
“Ina sa ran cibiyoyin da suka karÉ“i motocin za su É—auki cikakken alhakin kula da su, yadda ake amfani da su, gyaransu da kuma adana bayanan da suka shafe su. Shugabannin cibiyoyin za su É—auki alhakin duk wata É“arna, amfani da su ba bisa Æ™a’ida ba ko kuma lalacewar da za a iya kauce mata.

“Yayin da gwamnati ke Æ™ara zuba jari a fannin ilimi, dole ne mu gina al’adar kula da dukiyar gwamnati da É—aukar alhaki. Ya kamata dukiyar jama’a ta ci gaba da amfani ga jama’a har tsawon lokacin da aka tanade ta.

“Dole ne mu himmatu wajen samar da ingantaccen tsarin gudanar da aiki, tare da ba da muhimmanci ga gaskiya, riÆ™on amana da É—aukar alhaki.

“Gwamnatina za ta ci gaba da samar da gine-gine, kayan aiki da sauran tallafin da cibiyoyin ilimi ke buÆ™ata domin inganta ilimin gaba da sakandare a Zamfara. A madadin haka, muna sa ran samun shugabanci nagari, gudanar da dukiya cikin taka-tsantsan, da kuma ingantattun sakamako a fannin karatu da gudanar da harkokin makarantu.”

Gwamna Lawal ya kuma taya cibiyoyin da suka amfana murna, tare da buÆ™atarsu da su tabbatar da cewa motocin sun amfani cibiyoyin, É—alibai da al’ummar Jihar Zamfara baki É—aya, maimakon amfani da su wajen biyan buÆ™atun wasu mutane na Æ™ashin kansu.

No comments