Daga Zubairu M Lawal Gidauniyar dake fafutukar hadakan yan Najeriya wato (Advocacy for integrity and rule of law initiative) ta...
Daga Zubairu M Lawal
Gidauniyar dake fafutukar hadakan yan Najeriya wato (Advocacy for integrity and rule of law initiative) ta ratsar da Ko'odinetochi 20 a jihar Nasarawa.
Gidauniyar AIRLIN dake fafutukar hadakan yan kasa ta gudanar da taronta a zauren taro ta NUJ dake garin Lafia a ranar Asabar 20/7/2024.
Da yake jawabi ga manema labarai jin kadan bayan miqawa kodinetochin takardan kama aiki.
Shugaban Gidauniyar (Advocacy for integrity and rule of law initiative) Alhaji Muhammad Ibrahim Gamawa yace; makasudin samar da wannan gidauniyar shine yadda zasu hada kan yan kasa su fahince junansu.
Gamawa yace; zasu rika shirya taruruka a gurare dabam dabam domin wayarda kan al'umma ta yadda zasu fahinci juna saboda zaman lafiya.
Yace; duk rigingimun dake faruwa tsakanin al'umman Najeriya rashin fahintar junane. Idan aka fahinci juna kowa ya fahinci koyarwan addinin juna da koyarwan kabilun juna da sanin al'adu na zamantakewa da juna , zaisa mutani su zauna lafiya.
Alhaji Muhammad Ibrahim Gamawa: yace zasu cigaba da fadakar da matasa illolin shaye - shaye da yadda matasa ke hallaqar da kawunansu ko haukacewa cikin kuruciya.
Yace: zamu fadakar da mazauna unguwanni ta yadda zasu dakile yaduwar sayar da miyagun kwayoyi a unguwanninsu.
Yace; gidauniyar zata cigaba da wayarwa al'umma kai ta yadda zasu san yancinsu a guraren Shugabanni.
Yace: gidauniyar zata rika shurya taron kiyar da sana'o'in hannu ga mata da marayu da marasa galihu dama matasa.
Yace; wannan damace da kowani Dan qasa zaiyi amfani da ita wajen gina Najeriya da Muke ciki.
Yace; wadanan Ko'odinetochi sun fitone daga kananan Hukumomi 13 da yan-kuna 3 da ake dasu da kodinetochi na dalubai daga manyan makarantu.
Yace: ya zuwa yanzu wannan gidauniyar ta AIRLIN ta bude ofishinta a Bauchi gashi ta bude na biyu a Nasarawa zata garzaya zuwa Kaduna da Katsina da Nager da Jo's da sauran jihohin Najeriya.
Shugaban Gidauniyar ta jihar Nasarawa Alhaji Ibrahim Lawal Ibrahim yace: zasuyi aiki tukuru domin hadakan yan kasa su zama tsintsiya madaurinki daya.
Yace "aikine da ya rataya a wuyarmu mu gyara kasarmu, ta hanya fadakar da juna da taimakawa juna". Yace sun bude ofishinsu a rukuninrukunin kabtunan Plaza ta Kaura a cikin garin Lafia. Kuma suna samun mutani dake zuwa domin zama membobin kungiyar domin yin aiki tare.
Ko'odineta da ta fito daga karamar hukumar Wamba Mrs. Josephine Malle Augustine ta bayyana jin dadinta da ta samu kanta cikin Wanda zasubada gudumawa wajen hadakan yan kasa. Tace: zata shiga lungu da sako ta zakulo kwararu cikin musulmai da Kirista da zasuyi aiki tare.
Shima Malam Garba Bako da yafito daga karamar hukumar Toto yace: zai tabbatar burinshi ya cika ganin yan Najeriya sun hada kai sun sauna lafiya da juna.yace; yanzu haka yanada abokan aiki da zasu tabbatar al'umman yankinsu sun fahinci juna.
No comments