Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Majalisan zantarwa ta Shugabannin Kananan Hukumomin Najeriya ta kudduri aniyar tabbatar da zaman lafiya a yankunansu

Daga Zubairu M Lawal Lafia  Taron majalisan  zantarwa na Shugabannin Ciyamomin Najeriya wato (ALGON) ya maida hankali kan batun ...


Daga Zubairu M Lawal Lafia 

Taron majalisan  zantarwa na Shugabannin Ciyamomin Najeriya wato (ALGON) ya maida hankali kan batun matsalar tsaro da ya addabi al'umman Najeriya.

Taron ALGON karo na 48 da ya gudana a garin Lafia fadar jihar Nasarawa yafi maida hankali kan matsalar tsaro.

Taron da ya samu halartan manyan Shugabannin kananan Hukumomi daga jihohi 36 a tarayyar Najeriya ya janyo hankalin mahalartan yadda zasu gudanar da ayyukansu.

Cikin kasidar bayan taro da aka rabawa manema labarai, Shugabannin sunfi bada mahimmanci kan magance matsalar tsaro da ya addabi yan-kunan kananan Hukumomi a fadin kasar.

Sun bukaci maido da zaman lafiya a yan-kunansu domin Samar da harkan noma.

Sukace zaman lafiya shine kan gaba, da zai janyo kowani mataki na cigaba.

Haka zalika sun tattauna batun matsalar Samar da kananan Asibitochin sha katafi a yan kunan karkara domin taimakawa al'umman dake rayuwa  a karkara.

Sannan Samar da tsaftacecen ruwansha da zai taimakawa al'umma ta hanyar gina rijiyoyin burtsatse da sauransu.

Taron ya tabo batun aikin gona da zai taimaka wajen Samar da abinchi mai gina jiki da kuma lalubu hanyoyin fitar da abinci.

Haka zalika taron ya maida hankali kan batun Ilumin mazauna karkara. Ta yadda za a kula da gina makarantu saboda samar masu da ilumi da zai taimakawa rayuwarsu.

Tunda farko taron ya godewa Gwamnan jihar Nasarawa Engr. Abdullahi Sule saboda gudumawar da ya baiwa kungiyar ta yadda taron zai gudana.

Sukace Gwamnan ya tayasu murna saboda nasarar da suka samu a kotun koli.
Taron ya godewa Sarkin Lafia mai shari'a Sidi Muhammad Bage saboda kyakyawar tarba da yayi masu a lokacin da suka ziyarci fadarshi.

No comments