Inji Masana Daga Zubairu Lawal Lafia Ma'aikatan kiwon lafiya ta jihar Nasarawa ta shawarci al'umma dasu daina sanya Ka...
Inji Masana
Daga Zubairu Lawal Lafia
Ma'aikatan kiwon lafiya ta jihar Nasarawa ta shawarci al'umma dasu daina sanya Kansu cikin damuwa da dogon tunani saboda matsalar cutar lalurar kwakwalwa.
Da yake jawabi ga manema labarai Kwamishinan kiwon lafiya ta Jihar Dr. Gaza Gwamna Dogara yace; hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ware ranakun matsalar cutar kwakwalwa da ta cutar hukan kare, da sauran dabbobi.
Yace; saboda haka Ma'aikatan kiwon lafiya da ma'aikatan harkan noma da ta ruwansha suka shirya taron ranar cututukan, domin wayar da kan al'umma. Masana kiwon lafiya sukayi bayani domin kira ga al'umma dasu rika kula da kawunansu da duba lafiyan dabbobinsu.
Masan kiwon lafiya sun ce matsalar tattalin arziki da tsadar rayuwa na iya jefa ‘yan Najeriya da dama cikin yanayin fita daga hayyacin su, abinda ka iya shafar lafiyar kwakwalwarsu
Kamar yadda masana kiwon lafiyar bil Adama a jihar Nasarawa suka bayyanawa manema Labarai a taron wayar da kai na ranar lafiyan kwakwalwa ta duniya.
Kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Nasarawa da Dr. Gaza Gwamna Dogara yace; a a jihar Nasarawa an samu mutum 12 da suke fama da lalurar daga shekarar 2023 zuwa 2024
Rahotan ya ce cibiyoyin lafiyar Najeriya sun samu karin sama da kashi 200 na masu fama da irin wadannan matsaloli a Najeriya.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane sama da dubu 720 ke kashe kansu da kansu kowacce shekara a duniya saboda shiga irin wannan yanayi, kuma kashi 77 daga cikin su na fitowa ne daga kasashe matalauta da kuma masu tasowa irin Najeriya.
Masanan sun ce Najeriya ce gaba wajen samun mutanen da yanayin tsadar rayuwa ke shafar lafiyar kwakwalwar su.
An shawarci mutani dasu daina zama waje daya suna tunani marasa lisafi.
An gudanar da allurori ga karnuka na riga kafin cutar kwakwalwan karnuka.
No comments