Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP ta yi gargaɗi ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu mambobin jam’iyyar kan yunƙurin da zai iy...
Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP ta yi gargaɗi ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu mambobin jam’iyyar kan yunƙurin da zai iya lalata babban taron jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 ga Nuwamba, 2025.
Hakan na cikin sanarwar bayan taron gwamnonin karo na bakwai da aka gudanar a Gusau, Jihar Zamfara, ranar Asabar, 23 ga Agusta, 2025.
A cewar rahoton gidan talabijin na Channels, gwamnonin sun sake nanata goyon bayan su ga ƙudirin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na PDP karo na 101 da aka gudanar a watan Yuli, wanda ya amince da shirin babban taron jam’iyyar.
Taron na Gusau, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kuma tattauna kan halin da ƙasar ke ciki, matsalolin tsaro, raguwar darajar Dimokraɗiyya, da shirye-shiryen babban taron PDP mai zuwa.
Gwamnonin sun buƙaci mambobin ƙungiyar da su kaurace wa yunƙurin kawo cikas ga taron, inda suka bayyana jam’iyyar PDP a matsayin hanya ɗaya tilo wajen saita Dimokraɗiyya, kuma za ta iya maido da Nijeriya kan turbar shugabanci na-gari da ci gaba.
“Zauren ya sake tabbatar da cikakken ƙudurin da aka yi na taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 101 na Yuli 2025 dangane da babban taron ƙasa na ranar 15 ga Nuwamba.
“Muna kira ga mambobin ƙungiyar da su bijire wa duk wani yunƙuri na kawo cikas ga taron da masu adawa da jam’iyya ke yi; amma su ga jam’iyyar PDP a matsayin babbar cibiya ta Dimokraɗiyya da kuma hanyar maido da Nijeriya bisa tafarkin shugabanci nagari da ci gaban ƙasa,” inji wani bangare na sanarwar.
Taron wanda shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya jagoranta, ya tattauna sosai kan halin da al’umma ke ciki, rashin tsaro, rugujewar tsarin dimokuraɗiyya, da shirye-shiryen babban taron jam’iyyar na ƙasa da ke tafe.
Taron ya yaba da jajircewar shugabanni da mambobin jam’iyyar PDP wajen shawo kan makirce-makircen da aka ƙulla, inda ta jaddada cewa irin waɗannan abubuwan ba za su iya rusa farin jinin da jam’iyyar ba, da ƙoƙarin samar da sauƙin rayuwa da tsaro kamar yadda aka samu a ƙarƙashin gwamnatocin PDP.
Gwamnonin sun jaddada aniyarsu ta ceto ƙasar tare da zargin jam’iyyar APC da raba kan gwamnoni da manufofin da ke ci gaba da sanya ‘yan Nijeriya cikin halin ƙunci.
No comments