Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Lawal Ya Jagoranci Ƙaddamar Da Kwamitocin PDP Gabanin Babban Taron Jam’iyyar

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da kwamitocin tantancewa da na ayyuka na musamman na jam’iyyar PDP a ranar Juma’...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da kwamitocin tantancewa da na ayyuka na musamman na jam’iyyar PDP a ranar Juma’a, a shirye-shiryen gudanar da babban taron gangamin jam’iyyar mai zuwa.

An tsara babban taron zaben shugabannin jam’iyyar PDP na ƙasa (Elective National Convention) don gudana a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba, 2025.

Wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ta bayyana cewa an gudanar da bikin ƙaddamar da kwamitin tantancewa ne a Legacy House, Maitama, Abuja.

A yayin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal — wanda shi ne shugaban kwamitin tantancewa — ya bayyana cewa wannan kwamiti shi ne ginshiƙin da sahihin taron jam’iyyar zai ta’allaƙa a kai.

Ya ce, “Ga maza da mata da aka zaba don wannan kwamiti, ina yi muku maraba da girmamawa. An zabe ku ne ba don aiki na yau da kullum ba, amma don muhimmin aiki da ke da tasiri ga tsarin dimokuraɗiyyar mu. Ayyukan da kuke daf da fara aiwatarwa su ne tushe na tabbatar da gaskiya, tsari da nasarar wannan babban taro.

“Ayyukanku sun haɗa da samar da jerin sunayen wakilai na jam’iyya, littattafan taro, katunan shaidar shiga, da tabbatar da jin daɗin wakilai da baƙi. Wannan ba kawai aiki na gudanarwa ba ne, amana ce. Ku ne masu gadin mutuncin taron mu.”

Gwamnan ya ƙara da cewa, “Yayin da muke shirin wannan muhimmin tafiya ta cikin gida, ba za mu iya mantawa da cewa jam’iyyarmu tana tsallaka wani lokaci mai cike da ƙalubale ba. Don haka nake roƙonmu da mu yi aiki da gaskiya da haɗin kai domin ci gaban PDP.”

A yayin da yake ƙaddamar da kwamitin ayyuka na musamman a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Wadata Plaza, Abuja, Gwamna Lawal ya bayyana cewa wannan kwamiti yana da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nagartar taron.

Ya ce: “Ina taya ku murna da wannan aiki mai daraja. An zabe ku ne saboda kwarewarku, gaskiyarku, da aminci wajen gudanar da harkokin kuɗi. Ayyukanku sun haɗa da tsara daidaitattun kasafin kuɗi na ƙananan kwamiti, tara kuɗaɗe, sarrafa kashe kuɗi cikin gaskiya da bin doka, da kuma tabbatar da cewa kowanne kwamiti yana da kayan aikin da ake buƙata don nasarar babban taron.”

No comments