Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa matsalar rashin abinci mai gina jiki ba batun lafiya kaɗai ba ce, illa ce ta...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa matsalar rashin abinci mai gina jiki ba batun lafiya kaɗai ba ce, illa ce ta tattalin arziki da ke gurgunta ci gaban xan adam.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da Majalisar Habaka Abinci Mai Gina Jiki ta Zamfara (Zamfara State Council on Nutrition) da kuma Shirin Nutrition 774 Initiative a zauren Majalisar Zartarwa na gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Talata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa shirin Nutrition 774 Initiative wani tsari ne da ke tafiya ta matakin ƙananan hukumomi, mai haɗa sassa daban-daban na gwamnati, da nufin inganta lafiyar abinci a cikin ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.
Sanarwar ta ce, Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Zamfara za ta kasance mai jagorantar aiwatar da shirye-shiryen abinci mai ɗorewa a faɗin jihar.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ƙaddamar da wannan majalisa wata babbar dama ce da za ta inganta zamantakewar al’umma ta hanyar bai wa lafiyar yara muhimmanci.
Ya ce, “Ba za mu iya gina Zamfara mai kwanciyar hankali, juriya da ci gaba a kan tushe na rashin abinci mai gina jiki ba. Zuba jari cikin farkon kwanaki dubu xaya na rayuwar yaro shi ne babban jarin da za mu iya yi domin makomar jihar nan.”
Gwamnan ya ce, shirin Nutrition 774 Initiative ya zo a kan lokaci, kuma tsarin da yake amfani da shi na haɗin kai tsakanin sassa daban-daban kamar lafiya, noma, ilimi, da tsaftar muhalli (WASH) ya dace da manufar “Rescue Agenda” ta gwamnatinsa.
Ya ƙara da cewa, “Wannan shiri zai ƙarfafa yunƙurinmu na gida wajen inganta abinci mai gina jiki da kuma bai wa mata dama. Mun kafa cikakkiyar Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Zamfara, wacce ke da cikakken ikon tsara manufofi, tsara ayyuka, da kula da duk harkokin abinci mai gina jiki a faɗin jihar.”
Gwamna Lawal ya bayyana cewa babban aikin majalisar shi ne tabbatar da cewa shirin Nutrition 774 ya isa dukkan ƙananan hukumomi a jihar.
Ya ce, “Wannan ƙaddamarwa kira ce ga aiki. A shirye muke mu yi aiki tare da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, tare da tabbatar da horar da ma’aikata don gudanar da shirin cikin nasara. Gwamnatina za ta bayar da dukkan tallafi da jagoranci da ake buƙata domin tabbatar da ɗorewar shirin.”
Ya ƙare da cewa, “Da cikakken bege da nauyin da ke bisa mu, ina farin cikin ƙaddamar da Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Zamfara da kuma shirin Nutrition 774 Initiative a hukumance.”
A nata jawabin, Uju Rochas Anwukah, mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin lafiyar jama’a, ta yaba da jajircewar Gwamna Dauda Lawal wajen inganta harkokin lafiya, tana mai cewa shirin N774 Initiative na da nufin gina ƙasa mai cike da lafiya da ƙoshin gina jiki ta hanyar haɗa ƙoƙarin gwamnati daga matakin ƙasa har zuwa matakin ƙananan hukumomi.
No comments