Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kammala zagaye na goma na shirinta na musamman na aikin jinya kyauta, inda aka kula d...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kammala zagaye na goma na shirinta na musamman na aikin jinya kyauta, inda aka kula da marasa lafiya 3,447 daga sassa daban-daban na jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce shirin wanda aka fara shi tun watan Yuli na bara, yana bayar da jinyar kyauta ga marasa lafiya da ke fama da cuta irin su ciwon ido (cataract), kumburin mafitsara ko gambon ciki (hernia da hydrocele), da kula da masu yoyon fitsari na 'vesico-vaginal fistula' (VVF) tare da faxakar da jama’a kan kiwon lafiya.
An gudanar da zagayen jinya na goma a asibitoci kamar Asibutin Ƙwararru na Yariman Bakura, Babban Aaibitin Gusau, Aisbitin Ido na Gusau da Aaibitin Farida.
Sanarwar ta ce, “Domin rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta wajen samun kula da lafiya, gwamnatin Dauda Lawal ta Æ™addamar da wannan shiri na musamman domin tallafa wa masu Æ™aramin Æ™arfi da ke buÆ™atar jinya.”
Shirin, wanda aka fara a watan Agusta 2023, ya riga ya isa ga marasa lafiya sama da 3,400 zuwa asibitoci daban-daban ta hanyar tsarin tele-screening, wanda ke bai wa ƙwararrun likitoci damar lura da marasa lafiya daga ƙauyuka da yankunan karkara cikin gundumomi 14 na jihar.
Bangarorin da aka kula da lafiya a zagaye na goman da suka haÉ—a da; mutum 1,659 marasa lafiya masu kumburin ciki da irin sa. Mutum 1,081 masu ciwon ido da aka yi wa tiyata. Mutum 118 marasa lafiya masu cutar VVF da aka yi wa tiyata.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan shiri ya zama wata nasara ga gwamnatin jihar wajen kai ingantacciyar kulawar lafiya ga jama’a, musamman a yankunan da ke da Æ™arancin cibiyoyin jinya.
No comments