Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Lawal Ya Fara Ganawa Da Manyan Jiga-jigan PDP A Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buɗe ƙofar ganawa da manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a faɗin jihar, a wani yun...


Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buɗe ƙofar ganawa da manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a faɗin jihar, a wani yunƙuri na ƙarfafa haɗin kai da tsara makomar siyasa da ci gaban al’umma.

Taron farko na wannan shiri ya gudana ne ranar Talata a ɗakin taro na Rescue Hall da ke cikin Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara a Gusau. 

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa irin wannan ganawa na daga cikin matakan da jam’iyyar ke ɗauka akai-akai domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyya da kuma harkokin tafiyar da gwamnati a jihar.
A cewar sanarwar, an fara zagayen ganawar ne da wakilai da jiga-jigan jam’iyyar daga ƙananan hukumomin Gummi da Maru. An bayyana cewa wannan dandali na bai wa gwamnan damar tattaunawa kai tsaye da shugabannin jam’iyya a matakin jiha da na ƙananan hukumomi, tare da sauraron ra’ayoyinsu kan halin da ake ciki a yankunansu.

Sanarwar ta kara da cewa, a makonni masu zuwa, gwamnan zai karbi baƙuncin jiga-jigan PDP daga dukkanin ƙananan hukumomi 14 na jihar. Manufar hakan ita ce faɗaɗa tuntuba, ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnati da jam’iyya, da kuma tabbatar da cewa ana tafiya tare da ra’ayoyin al’umma wajen ɗaukar matakai.
A yayin waɗannan taruka, ana bai wa mahalarta dama su gabatar da ƙorafe-ƙorafe, shawarwari da kuma nazari mai ma’ana kan al’amuran da suka shafi siyasa, tsaro, da ci gaban jama’a a yankunansu. Hakan na taimakawa gwamnati wajen fahimtar halin da ake ciki a matakin ƙasa, tare da tsara hanyoyin magance ƙalubale cikin haɗin gwiwa.

No comments