Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

DA ALAMUN WASU JIGA-JIGAN JAM’IYYAR APC A JIHAR KATSINA ZA SU YI ANTI-PARTY

Daga Awwal Jibril Yankara Da alamu wasu jiga-jigan Jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Faskari ta Jihar Katsina za su yi abin da ake...


Daga Awwal Jibril Yankara

Da alamu wasu jiga-jigan Jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Faskari ta Jihar Katsina za su yi abin da ake kira anti-party a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
Musamman a kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya (House of Representatives), inda tsohon Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina, Hon. Hamza Sulaiman Faskari (Wamban Faskari, Sadaukin Ƙasar Hausa na 1), zai tsaya takarar ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC.
Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar sun kasa ɓoye manufarsu cewa idan Allah Ya kai su zaɓen 2027, za su yi anti-party.
Daga cikinsu akwai Hon. Bishir Wada Faskari, wanda ake zargin yana bayyana ra’ayinsa a fili ba tare da jin tsoro ko kunya ba. Kuma ba shi kaɗai ba ne, domin akwai wasu da dama a cikin APC a yankunan Kankara, Faskari da Sabuwa da ake dangantawa da irin wannan ra’ayi.
Mafi yawansu dai na tare ne da Hon. Shehu Dalhatu Tafoki, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kankara, Faskari da Sabuwa, wanda ya fice daga APC zuwa PDP, inda ake sa ran zai sake neman kujerarsa a ƙarƙashin sabuwar jam’iyyarsa.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin magoya bayansa kan faɗi a fili cewa:
Najeriya sai Tinubu
Katsina sai Dikko
Funtua Zone sai Dan Dutse
Amma Kankara, Faskari da Sabuwa sai PDP
Wannan ne ake gani a matsayin babban ƙalubale ga ɗan takarar APC, Hon. Hamza Sulaiman Faskari.
Masu wannan korafi sun sha alwashin cewa ko da za a kore su daga jam’iyyar, ba za su fita da kansu ba.
Rahotanni sun nuna cewa irin wannan yanayi na faruwa a wasu sassan Kankara da Sabuwa ma. Sai dai lokaci ne kaɗai zai bayyana yadda al’amura za su kasance.
A wani bincike da muka gudanar, mun gano cewa wasu daga cikin masu wannan ra’ayi na da hujjojin da suke ganin suna da ƙarfi, yayin da wasu kuma ke danganta matsalolin da rashin lallashi da rashin ba su muhimmanci daga wasu makusantan Hon. Hamza.
Wasu daga cikin masu korafin sun bayyana cewa, idan za a gudanar da wani taro, sau da yawa sai dai su ji labari ko kuma su zo da kansu saboda kishin da suke yi wa Hon. Hamza Sulaiman Faskari.
Sun ce irin wannan yanayi yana rage musu kima a siyasa, tare da ba wasu damar raina su ko sukar gudummawar da suke bayarwa. A cewarsu, ana nuna kamar ko suna nan ko babu ba wani tasiri suke da shi ba.
Wani dattijo daga Yankara, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa akwai mutanen kirki irin su Injiniya Murtala Ibrahim Sheme da Hon. Bala Ado da har yanzu suke ƙoƙarin daidaita tafiyar siyasar.
Ya ƙara da cewa da ba don irin waɗannan mutane ba, da tuni matsalar ta fi haka muni.
A cewarsa, mafi yawan masu korafin a faɗin ƙaramar hukumar Faskari sun fi bai wa Injiniya Murtala Ibrahim Sheme muhimmanci, domin suna ganin shi mutum ne mai iya haɗa kai da kuma taimakon jama’a.
Sun yi kira gare shi da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin ƙarfafa tafiyar siyasar Hon. Hamza Sulaiman Faskari, maimakon a bar rikice-rikice da rashin fahimta su kassara tafiyar tun kafin zaɓe ya zo.
A ƙarshe, masu wannan kira sun jaddada cewa yanzu lokaci ne na rarrashi, haɗin kai da girmama juna, ba lokacin nuna iko ko fifiko kusa da shugabanni ba.
Sun ce idan ana son a taimaki Wamban Faskari ya samu nasara, dole ne a bai wa kowa muhimmanci tare da haɗa kan dukkan masu ruwa da tsaki.

No comments