Daga Ibrahim Muhammad Kano Mai Kula da Shirin "YEIDEP'S Financial Partners" na Jihar Yobe, Hon. Hassan Kaku Hassan...
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Mai Kula da Shirin "YEIDEP'S Financial Partners" na Jihar Yobe, Hon. Hassan Kaku Hassan, ya ce babbar manufar shirin ita ce taimaka wa matasa su samu abin yi domin su zama masu dogaro da kansu. Wannan shi ne kuma burin Gwamnatin Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da hadin gwiwar Gwamnoni na kasar nan baki daya.
Hon. Hassan Kaku Hassan ya bayyana hakan ne yayin taron kaddamar da shirin a jihar Kano.
Ya ce shirin zai yi tasiri kai tsaye a tsakanin al’umma, domin an tsara shi ne tallafin ya shiga hannun al’umma kai tsaye ba tare da wani nuku-nuku ba.
"Duk wanda ya bude asusun ajiya na Banki kuma an saka lambar sa cikin tsarin, duk lokacin da aka bayar da tallafi zai shiga cikin asusun sa kai tsaye," in ji shi.
Ya kara da cewa sannan za a yi wa matasa horo kan sana’o’i daban-daban. Ya ce hakan zai taimaka wajen dakile irin munanan ayyukan da wasu matasa ke shiga a kasar nan. Don haka ne Gwamnati ta ga dacewar fito da irin wadannan tsare-tsare da za su hana matasa fadawa ayyukan da basu dace ba.
Hon. Hassan ya ce rashin ilimi da rashin aikin yi na daga cikin manyan abubuwan da ke jawo matasa su fada cikin halaye marasa kyau. Ya ce wannan shirin an tsara shi ne domin hana matasa maza da mata shiga shaye-shaye ta hanyar samar musu da ayyukan yi. Wannan ce babbar manufar shirin a fadin kasar nan.
Ya bayyana cewa masu shirin "YEIDEP'S Financial Partners" na sa ran shirin zai samu karbuwa sosai a tsakanin matasan Jihar Yobe. Ya ce za su yi ta wayar da kan al’umma kan muhimmancin shiga shirin ta hanyar bude asusun ajiya a bankuna.
A ƙarshe ya yaba da yadda shirin ke tafiya yadda ya kamata a Jihar Kano karkashin jagorancin Shugaban shirin na Arewa baki daya, Hon. Sani Musa Danja, Mai Ba Gwamnan Kano Shawara kan Harkokin Matasa da Wasanni, bisa goyon bayan da ya bayar.
Hon. Hassan Kaku Hassan ya yi kira ga al’umma cewa duk wanda tallafin ya shiga hannunsa ya yi amfani da shi ta yadda zai amfana kansa, yan’uwa, makwabta da jihar sa baki ɗaya.
No comments