Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Jimamin Rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Mai Martaba Alhaji Bello Sul...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman.

Mai martaban ya rasu ne a ranar Litinin a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Talata, Gwamna Lawal ya bayyana rasuwar Sarkin a matsayin babban rashi ga iyalansa, Masarautar Zurmi, harkokin gargajiya da kuma al’ummar Jihar Zamfara baki É—aya.

Gwamnan ya ce rasuwar Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman ta girgiza shi matuĆ™a, yana mai cewa za a riĆ™a tunawa da Sarkin bisa irin hidimar da ya yi wa al’ummarsa, gudunmawar da ya bayar wajen Ć™arfafa masarautun gargajiya da kuma Ć™oĆ™arinsa na ganin an samu zaman lafiya da ci gaban Jihar Zamfara.

“Ina matuĆ™ar baĆ™in ciki da rasuwar Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman, Sarkin Zamfaran Zurmi.

“Rasuwarsa babban rashi ne ga Jihar Zamfara. Za a riĆ™a tunawa da shi bisa hidimar da ya yi wa al’ummarsa, gudunmawar da ya bayar ga masarautar gargajiya da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jiharmu,” inji Gwamna Lawal.

Ya Ć™ara da cewa, a madadin Gwamnatin Jihar Zamfara da al’ummar jihar, yana miĆ™a saĆ™on ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Zurmi da É—aukacin al’ummar Masarautar Zurmi.

Gwamnan ya roĆ™i Allah MaÉ—aukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya saka masa da alheran da ya aikata, Ya ba shi Aljannar Firdausi, tare da bai wa iyalansa da al’ummar Zurmi haĆ™urin jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.

No comments