Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu'annati ta Nijeriya (EFCC), Olanipekun Olukoyede, ya bayyana cew...
Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu'annati ta Nijeriya (EFCC), Olanipekun Olukoyede, ya bayyana cewa jihar Zamfara ta samu sauyi mai ma’ana a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal.
A wata sanarwa da Sulaiman Bala Idris Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara ya fitar, ya ce, Olukoyede ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da babban jawabi a bikin cika shekaru 30 da kafuwar jihar Zamfara, wanda aka gudanar a babban zauren taro na Gidan Gwamnatin Jihar da ke Gusau.
Sauran fitattun masana da suka gabatar da jawabai a wajen taron sun haɗa da Farfesa Tijjani Muhammad Bande, Farfesa Sulaiman Kura, Farfesa Murtala Rufai da Farfesa Taofik Aminu, da wasu.
Shugaban EFCC ya ce, kafin ya amince da gayyatar da aka yi masa domin gabatar da babban jawabi a bikin, sai da ya gudanar da bincike kan jihar Zamfara da kuma gwamnan jihar, domin sanin irin ayyukan da ake gudanarwa a can.
Ya ce, bisa ƙa’idojin ɗabi’a da aikinsa na shugaban EFCC ya ɗora masa, ba ya halartar tarukan siyasa ko zuwa gidan gwamnati. Sai dai ya ce gayyatar da aka yi masa a wannan karon ta sa ya ji ya kamata ya amince da ita domin ganin irin abubuwan da ke faruwa a jihar.
Olukoyede ya bayyana cewa bayan binciken da ya gudanar, ya lura da manyan sauye-sauyen da jihar ta samu cikin shekaru uku da suka gabata, tun bayan ƙirƙirarta. Hakan ne ya sa ya yanke shawarar amincewa da gayyatar, inda ya je ya sanar da Shugaba Bola Tinubu abin da ya gano tare da bayyana masa muhimmancin tallafa wa ayyukan Gwamna Dauda Lawal.
Ya ce ya yi matuƙar farin cikin kasancewa a Zamfara, yana mai cewa wannan ce ziyararsa ta farko a jihar, kasancewar ofishinsa na Abuja ne kuma aikinsa ba kasafai yake kai shi wannan ɓangaren ƙasar ba.
Shugaban EFCC ya ce tun daga lokacin da ya isa Gusau, sabon filin jirgin saman jihar ne abu na farko da ya ja hankalinsa. Ya ƙara da cewa sauye-sauyen da ake gani a babban birnin jihar sun haɗa da sabbin hanyoyi da aka shimfiɗa tare da fitilun hasken rana da aka girka a gefensu.
Ya bayyana cewa a baya Zamfara ta kasance cikin jihohin da ke ƙasan jerin jihohin ƙasar wajen ci gaba, ba don rashin albarkatun ƙasa ko kyawawan wurare ba, sai dai saboda yadda wasu ra’ayoyi kan tsauraran al’adun zamantakewa suka mamaye tunanin jama’a, lamarin da ya rufe irin damar ci gaban da jihar ke da ita.
Olukoyede ya ce ko bayan zama babban birnin jiha a shekarar 1996, sauyin da ake buƙata bai samu cikin gaggawa ba. Ya bayyana cewa tsawon shekaru, duk da ƙoƙarin gwamnonin da suka gabata, Zamfara ta ci gaba da kasancewa cikin jihohin da ba su samu ci gaba sosai ba.
Sai dai ya ce a halin yanzu ana samun sauyi a yanayin jihar, inda ci gaban da ake gani a Gusau ke zama wata alama ta sauye-sauyen da ke gudana a faɗin Zamfara baki ɗaya.
Ya kuma bayyana jin daɗinsa kan yadda jihar ke samun ci gaba a sakamakon jarrabawar manyan makarantun sakandare na ƙasa, musamman jarrabawar Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare ta Ƙasa (NECO) da kuma Hukumar Shirya Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC).
A cewarsa, ana kuma faɗaɗa gine-ginen more rayuwar jama’a, lamarin da ke taimaka wa al’umma a harkokinsu na yau da kullum. Ya danganta waɗannan nasarori da ƙoƙarin gwamnatin jihar na aiwatar da sauye-sauye bisa tsari da manufa.
Ya ce nasarorin sun yi daidai da taken laccar bikin na bana, mai cewa: “Riƙon amana da ɗaukar nauyi a tafiyar da gwamnati mai kawo sauyi.”
Shugaban EFCC ya ƙara da cewa, duk da ƙa’idojin ɗabi’a da ofishinsa ke buƙata, sai gwamna mai kishin dimokuraɗiyya, gaskiya da riƙon amana ne zai iya samun ƙarfin halin gayyatar shugaban EFCC domin ya yi wa al’ummar jiharsa jawabi.
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya ce taken bikin na bana, “Tunani kan Abubuwan da Suka Gabata, Nasarorin da Aka Cimma da Kuma Makomar Gaba,” an zaɓe shi ne domin duba ƙalubalen da suka tsara tarihin jihar tare da nazarin matakan da shugabanni ya kamata su ɗauka domin samar da kyakkyawar makoma.
Gwamnan ya bayyana jin daɗinsa kan yadda bikin ya wuce matsayin shagulgula kawai, inda ya samar da tattaunawa mai zurfi kan muhimman batutuwan da suka shafi al’umma da shugabanci.
Ya ce takardun nazari da aka gabatar a wajen taron sun mayar da hankali kan muhimman nauyin da ke kan gwamnati, waɗanda suka haɗa da riƙon amana a harkokin gwamnati, shigar al’umma cikin yaƙi da rashin tsaro, kiyaye tarihi da al’adu, da kuma dangantakar da ke tsakanin tsaro da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Lawal ya ce waɗannan batutuwa suna daga cikin ginshiƙan ayyukan gwamnatinsa. Ya bayyana cewa Tsarin Ceto na Matakai Shida da gwamnatinsa ta ƙaddamar yana da nufin magance manyan ƙalubalen jihar.
Ya kuma ce Tsarin Bunƙasa Jihar Zamfara na shekarar 2025 zuwa 2034 ya tanadi hanya mai dogon zango wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, inganta walwalar jama’a, bunƙasa ƙwarewar al’umma, kyautata shugabanci da kuma kiyaye muhalli.
Gwamnan ya jaddada cewa wajibi ne gwamnati ta tabbatar da cewa waɗannan tsare-tsare sun haifar da sauye-sauye na zahiri waɗanda jama’a za su iya gani kuma su amfana da su a rayuwarsu.
A ƙarshe, ya gode wa dukkan waɗanda suka gabatar da takardun nazari bisa gudummawar ilimi da ƙwarewar da suka kawo wajen taron. Ya kuma miƙa godiyarsa ga shugaban taron, masu sharhi kan takardun, kwamitin shirya bikin da kuma ƙaramin kwamitin kula da lacca da wallafe-wallafe, tare da sauran baƙi da mahalarta taron.

No comments