Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

SHEKARU 20 A KARAGA: Sarkin Musulmi Ginshiƙi Ne Na Haɗin Kai Da Zaman Lafiya, In Ji Gwamna Dauda

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a matsayin shugab...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a matsayin shugaba mai tawali’u wanda ke haɗa kan al’umma tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Gwamna Lawal ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya halarci taron Makon Sheikh Usmanu Ɗan Fodiyo karo na 13, da kuma bikin cika shekara 20 da naɗin Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III a matsayin Sarkin Musulmi. 

An gudanar da taron ne a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa da ke Sakkwato.

An gudanar da bikin na bana ne ƙarƙashin taken: “Farfaɗo da Jagoranci Mai Kyawawan Ɗabi’u da Zaman Lafiyar Al’umma: Darussan da za a Koya daga Shugabannin Jihadin Sakkwato.” Taron ya samu halartar manyan mutane daga Nijeriya da sauran ƙasashe.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Sulaiman Bala Idris, Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, a ranar 3 ga Nuwamba, 2026.

A saƙon taya murna da ya gabatar, Gwamna Lawal ya ce hikima, shawarwari da jajircewar Sarkin Musulmi wajen jagoranci sun kasance abin koyi da ƙarfafa gwiwa ga gwamnatin Jihar Zamfara da al’ummarta, musamman a lokutan da ake fuskantar matsalolin tsaro da ƙalubalen zamantakewa.

Ya ce, “Cike da farin ciki, girmamawa da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, a madadin gwamnatin Jihar Zamfara da al’ummarta, ina taya Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmi na 20 kuma jagoran al’ummar Musulmi, murnar cika shekara 20 da hawansa karagar sarautar Sarkin Musulmi. Wannan babban lamari ne na tarihi.

“Muna matuƙar godiya da ziyararku da goyon bayan da kuka ba mu a lokacin bikin naɗin sarakunanmu da miƙa musu sandunan ikon sarauta a Gusau. Wannan ya ƙara tabbatar da jajircewarku wajen ƙarfafa hukumomin gargajiya a yankinmu.

“Bikin na bana ya tunasar da mu cewa gadon tarihi da Daular Usmaniyya ta bari ya wuce iyakokin ƙasa. Ƙimomin da ta gada na ilimi, adalci, tarbiyya, jagoranci nagari da mutunta ɗan Adam har yanzu suna da matuƙar muhimmanci wajen tunkarar ƙalubalen da muke fuskanta a yau.

“Musamman a Jihar Zamfara, wannan gado yana ɗauke da saƙo mai muhimmanci. A daidai lokacin da matsalar rashin tsaro, tabarbarewar ɗabi’u, talauci da kuma barazanar da ke fuskantar matasa ke addabar al’ummominmu, wajibi ne mu yi koyi da koyarwar Sheikh Usmanu Ɗan Fodiyo wajen bunƙasa zaman lafiya, adalci, ilimi da ɗaukar nauyin al’umma.”

Tun da farko, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya gode wa dukkan waɗanda suka taka rawa tare da bayar da gudummawa a tsawon shekaru 20 da ya shafe a kan karagar sarautar.

Ya kuma yi kira ga shugabannin addinai, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da su ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan da za su inganta zaman lafiya.

No comments