Daga Hussaini Yero, Gusau Ɗaya daga cikin jigo a jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Sani Abdullahi, Wamban Shinkafi ya yi...
Daga Hussaini Yero, Gusau
Ɗaya daga cikin jigo a jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Sani Abdullahi, Wamban Shinkafi ya yi zargin cewa wasu 'yan siyasa masu yi ma gwamnatin jihar Zamfara, ƙarƙashin Jagorancin Gwamna Dauda Lawal Zagon ƙas, suna shirin cimma burin su na siyasa, inda suke kiran Gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta-baci a Zamfara.
Wamban Shinkafi ya bayyana haka ne a zantawar sa da manema labarai a Gusau, babban Birnin Jihar Zamfara a makon nan.
A cewar sa, kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya a bayyane yake, wanda ya rufe ido ne kawai ba zai iya fahimtar me ake nufi ba.
"Bari in faɗi a fili cewa Zamfara ba ta cancanci a ayyana dokar ta-ɓaci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada ba. Ya kamata masu ɗaukar nauyin su su je su karanta da kyau su fahimci abin da tsarin mulki ya ce." Ya ce.
Ya bayyana cewa sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima yana magana ne kan ayyana dokar ta-ɓaci musamman ma, ta zayyana sharuɗɗan da shugaban zai iya ayyana dokar ta-ɓaci da kuma hanyoyin da ya kamata a bi.
Ya ce, "A ɗauki misali da Borno inda aka kashe dubbai, wasu kuma suka yi gudun hijira daga Benue, Taraba, Neja da sauran jihohin da ake fama da rashin tsaro, ba mu taba jin wani ya fito daga waɗannan jihohin ya yi irin wannan kiran ba, sai a Zamfara?"
Daga nan Wamban na Shinkafi ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa ne ke son kawo tabarbarewar zaman lafiya a Zamfara, shi ya sa suka ɗauki nauyin ‘yan gudun hijirar domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da rashin tsaro a jihar, wanda Gwamna Dauda Lawal ya gada daga gwamnatin da ta gabata a jihar.
"Kira da kafa dokar ta-ɓaci a Zamfara aiki ne na 'yan siyasa da ke gudun hijira daga jihar, suna son su durkusar da jihar ne don neman cimma burin su na siyasa," ya faɗa.
Ya kuma yi zargin cewa akwai maƙiya a ciki, waɗanda ke taimaka wa ayyukan ‘yan bindiga, wanda ya shawarci hukumomin tsaro a jihar da su haskaka idanun su, su kuma yi taka-tsantsan kan masu zanga-zangar.
Jigon na APC ya ƙara da cewa, maƙiyan Zamfarawa ne ke ta ƙoƙarin sun tarwatsa ci gaban da ake samu a jihar ƙarƙashin Jagorancin Gwamna Dauda Lawal da Shugaban ƙasa Bula Ahmad Tunubu.
"Don haka Jama'a su yi hattara da waɗannan 'Yan barandan Siyasa waɗanda fatar su ita ce tarwatsa jihar Zamfara ba ci gaban ta ba," ya ƙarƙare.
No comments