Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jinjina wa ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe, Hon. Kabiru Ahmadu Mai...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jinjina wa ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe, Hon. Kabiru Ahmadu Mai Palace, bisa rawar da ya taka wajen inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ƙaddamarwa, sabuntawa tare da faɗaɗa Cibiyar Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Dakta Karima da ke Tudun Wada a Gusau, babban birnin jihar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, aikin na daga cikin ayyukan mazaba na shekarar 2025 da Hon. Mai Palace ya aiwatar.
Sanarwar ta nuna cewa, an faɗaɗa cibiyar kiwon lafiyar daga gadon marasa lafiya guda 10 zuwa gadaje 40, tare da samar da ƙarin kayan aiki na zamani domin inganta ayyukan jinya da kula da lafiyar al’umma.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana gamsuwarsa da ci gaban da ake samu a bangaren lafiya, yana mai cewa ƙoƙarin san majalisar ya dace da manufofin gwamnatinsa na Shirin Ajanda Shida.
Ya ce, ƙoƙarin da ake yi a ɓangaren lafiya a jihar ya haɗa da samar da magunguna masu muhimmanci, ƙarfafa matakan rigakafi, sabunta manufofin lafiya, tsaftar muhalli, kula da masu juna biyu da yara, da kuma bunƙasa hanyoyin samar da kuɗaɗen tafiya da bangaren lafiya.
Gwamnan ya jaddada cewa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauƙi ga al’umma, domin su ne matakin farko da jama’a ke samun kulawar lafiya kafin a tura su manyan asibitoci.
Haka kuma, ya yaba da sauran ayyukan da Hon. Mai Palace ke aiwatarwa a fannin lafiya da ilimi, ciki har da gina cikakken ɗakin kwantar da marasa lafiya a wata cibiyar lafiya da ke Gusau da kuma gyaran gine-gine a babban asibitin Magami.
Ya kuma ambaci ayyukan gina ajujuwa da cibiyar jarrabawar kwamfuta (CBT) da ɗan majalisar ke yi a wasu makarantu.
A nasa jawabin, Hon. Kabiru Ahmadu Mai Palace ya gode wa gwamnan bisa halartar ƙaddamarwar, yana mai cewa irin waɗannan cibiyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen samar da kulawar gaggawa ga al’umma, lamarin da ya sa ya mayar da hankali kan bangaren lafiya a ayyukan mazabarsa.
Ƙaddamar da cibiyar, a cewar gwamnatin jihar, na nuna haɗin gwiwa tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa wajen kawo ci gaba kai tsaye ga rayuwar jama’a a matakin ƙasa.
No comments