Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙalubalanci Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan ya fito fili ya bayyan...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙalubalanci Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan ya fito fili ya bayyana matsayin sa na siyasa dangane da alaƙar sa da haɗakar RAINBOW, gabanin babban zaɓen 2027.
Wike, wanda mamba ne a Jam’iyyar PDP, yana cikin ’yan siyasar da ke da alaƙa da haɗakar RAINBOW, wata ƙungiyar siyasa mai haɗa jam’iyyu daban-daban da ke tattara goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Sai dai wannan al’amari ya jawo adawa daga wasu gwamnonin APC, waɗanda suka ce za su mara wa Tinubu baya tare da sauran ’yan takarar da za su fafata a ƙarƙashin tutar APC.
Da yake magana a wata hira da shirin 'Inside Sources' na Channels a gefen taron Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da aka gudanar a New York, Lawal ya ce Wike ba zai iya goyon bayan APC da wasu jam’iyyu daban-daban a lokaci guda ba, yana mai cewa dole ne ya bayyana inda amincin sa na siyasa yake.
“Saƙon mu a bayyane yake ƙwarai. Ka tsaya a gefe guda, ba za ka iya kasancewa a ɓangarori biyu ba. Idan kana cikin APC, to ka fito fili ka mara wa APC baya, ba wai kana goyon bayan APC a nan sannan kana goyon bayan wasu jam’iyyun siyasa a wani wuri ba,” in ji shi.
Lawal ya ce gwamnonin APC ba za su sauya matsayin su ba, duk da ci gaba da kare ƙawancen RAINBOW da Wike ke yi da kuma goyon bayan da yake bai wa sake zaɓen Tinubu.
“Mun tsaya kan matsayim mu, kuma saƙon a bayyane yake. Zai iya magana, zai iya faɗin duk abin da yake so, amma matsayin mu a bayyane yake, APC gaba ɗaya daga sama har ƙasa,” in ji gwamnan.
Da aka tambaye shi ko matsayin gwamnonin APC yana nufin suna buƙatar Wike ya koma jam’iyyar APC, Lawal ya amsa da cewa: “Daidai ke nan.”
Gwamnan na Zamfara ya kuma bayyana cewa zai tattauna da Shugaba Tinubu kan matsayin Wike na siyasa bayan dawowar Shugaban Ƙasar daga hutun aikin sa a Faransa.
“Wannan wani abu ne da zan tattauna da Shugaban Ƙasa idan ya dawo. A bayyana mana inda wannan mutum yake. Ko yana cikin APC ko ba ya ciki, abu mai sauƙi ne. Don haka zan bi ’yan uwana, sauran gwamnonin,” in ji Lawal.
Wannan kalamai sun biyo bayan matsayar Ƙungiyar Gwamnonin APC (PGF) da ta yi watsi da duk wata ƙawance ko yarjejeniyar siyasa da take ganin za ta iya raunana APC ko ’yan takararta a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta bayyana cewa mambobinta za su mara wa Tinubu baya, tare da goyon bayan ’yan takarar APC a dukkan matakan zaɓe.
Sai dai Wike ya sha nanata cewa goyon bayan da yake bai wa sake zaɓen Tinubu ba yana nufin ya yi yarjejeniya da APC ba, kuma ba ya hana sauran jam’iyyun siyasa tsayar da ’yan takararsu a zaɓen gwamna da na majalisun dokoki.
Da yake magana da ’yan jarida a Abuja ranar Litinin, 21 ga Satumba, bayan duba wasu ayyukan gina hanyoyi da ake gudanarwa a FCT, Wike ya sake jaddada cewa tabbatar da sake zaɓen Tinubu shi ne babban abin da ya fi mayar da hankali a kansa a siyasa.
Ya kuma yi watsi da zargin cewa an kafa Kawancen Rainbow ne domin tarwatsa ko raunana jam’iyyun siyasa da suke da yanzu.
Ministan FCT ya ce ’yan jam’iyyu daban-daban za su iya goyon bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa, yayin da suke ci gaba da riƙe kasancewarsu a jam’iyyunsu tare da goyon bayan ’yan takarar wasu jam’iyyu a sauran zaɓuka.
Wike ya kuma ci gaba da nuna goyon baya ga ’yan takarar PDP a zaɓen 2027 a wasu jihohi, ciki har da Imo da Kwara, lamarin da ya ƙara ruruta takaddamar kan ko goyon bayan Tinubu zai iya tafiya tare da goyon bayan ’yan takarar wasu jam’iyyu.
Sabani tsakanin Wike da wasu gwamnonin APC ya ta’allaka ne kan ko Kawancen Rainbow zai iya ci gaba da gudanar da ayyukansa tare da tsarin yaƙin neman zaɓen APC, yayin da mambobinsa ke ci gaba da kasancewa cikin wasu jam’iyyun siyasa.
Wike na cewa manufar kawancen ita ce tattara goyon baya ga Tinubu ne, yayin da gwamnonin APC ke buƙatar a samu tsarin yaƙin neman zaɓe guda ɗaya da ya ta’allaka kan jam’iyyar da kuma ’yan takararta.
No comments