Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin 'Yan Ta'adda, Amma Ba Sasanci Ba -Mataimakin Gwamnan Zamfara

Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara, Mani Malam Mumini ya ƙara jaddada matsayar gwamnatin su na rashin amincewa da sasanci da '...

Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara, Mani Malam Mumini ya ƙara jaddada matsayar gwamnatin su na rashin amincewa da sasanci da 'yan bindiga da sauran miyagu, yana mai cewa ɗaukar tsattsauran matakin soji na ruwan wuta ne kawai mafita.

Malam Mumini ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin na tabbatar da ganin ta kawo ƙarshen rashin tsaron da ya addabi jihar, tare da yin alƙawarin ƙaro jami'an tsaro a yankin Banga, inda 'yan ta'adda suka kashe mutum 38 bayan da suka yi garkuwa da su.

Mataimakin Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wata ziyarar jaje sakamakon wani mummunan aiki na 'yan bindigar da ya auku a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.

Sakamakon wannan mummunan ta'annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma'aikatan gwamnati da jami'an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe.

Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al'ummu cewa gwamnatin na nan tana duk abin da za ta iya yi don kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin.

Lokacin da ya ke mayar da jawabi, shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, Manir Haidara ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin ta samar da tsaro a duk faɗin jihar Zamfara.

No comments